![]() |
| Taswirar tsibirin bermuda kenan |
Takaitaccen bayani game da Bamuda Triangle
Menene tsibirin Bermuda, a ina tsibirin bamuda yake kuma me yasa wannan tsibiri yake da hatsari?
Wadannan sune tambayoyin da a ke yawaita yi ko suke darsuwa a ran mutum duk sa'adda a ke batun wannan tsibirin halaka.
To labarin da muke ji na tsibirin Bamuda an fara shi ne yau kusan shekara 57 kenan tun a shekarar 1964.
Wani marubuci ba'amurke Vincent Gaddis shine ya fara ayyana sunan wannan waje mai hatsari da sunan Tsibirin Bamuda wato Bermuda Triangle a turance. Bayan haka kuma wasu marubuta suna masa lakabi da tsibirin shaidan Devil's island(wato suna ganin cewa a wannan waje ne fadar shaidan take wato iblis).
Abinda yasa wannan tsibiri yake da hatsari kuwa shine
Wannan bigire duk abinda ya ratsa ta cikinsa to sai dai a neme shi a rasa ko sama ko bisa Allahu a'alamu, jiragen ruwa da jiragen sama da dama sun hallaka a wannan tsibiri sun bace bat babu labarinsu har gobe. Masana da dama sunyi rubuce-rubuce da kuma bincike mai fadi domin gano musabbabin abinda ke faruwa a wannan tsibiri amma har yanzu sun kasa gano ko menene.
A ina tsibirin Bermuda yake
To shi dai wannan wuri da ake kira da suna bamuda triangle, wani yanki ne da ake siffanta shi da kusurwowi guda uku a cikin tekun Atlantika a kasar Amurka, kuma yana nan ne a daura da kudancin gabar tekun, wanda ya hada da wani bangare daga tsibirin Bahama da Puerto-rico, da wani yanki na jihar Florida, da kuma shi kansa tsibirin bamuda wanda wannan wuri ya samo sunansa daga gareshi.
Kamar yadda bayani ya gabata jiragen ruwa da kuma na sama da dama sun halaka sun bace bat sakamakon kokarin ratsawa ta wannan wuri na bamuda.
![]() |
| Yadda jiragen ruwa ke hallaka a tsibirin bamuda yayinda ruwa ya soma hankoro sai ya fara murdewa yana jan duk abinda ya matso kusa. |
Wata mujalla da ake kira da suna “national geographic magazine’’ ta bayyana wannan yanki na bamuda a matsayin al'amari mafi girma kuma mafi rikitarwa da aka kasa fahimtarsa a wannan zamani, akwai jirage da dama da suka halaka a wannan wuri, misali a ranar 8 ga watan Janairun 1962 wani jirgin sama da ake kira da suna Aerial tanker kirar kb50 ya bace bat sakamakon bi ta sararin samaniyar wannan wuri, an kuma neme shi ko sama ko kasa har yau ba aji duriyarsa ba.
Duk da cewa a wancan lokaci kafafen yada labarai da dama sun bayar da rahoton cewa wannan jirgi ya yi hadari ne a sama sannan kuma ya fado ya nutse a cikin teku.
Sai dai sakamakon cikakken bincike da aka gudanar ya musanta wadannan rahotanni na kafafen yada labarai, domin kuwa babu wata hujja daya tilo da ta tabbatar da hakan.
KARANTA WANNAN: ► Bayani Game Da Blackhole
Kuma wannan ba ita ce bacewa ta farko kuma ta ban al'ajabi ba, domin kuwa tun kafin wannan ta auku akwai wadansu jiragen guda biyu da suka hadu da irin wannan garari.
Farkon abinda yasa sunan Bermuda ya kara shahara shine na batan Jirage na Flight 19 mallakar jami'an hukumar sojojin ruwa wato Navy na TBM "avengers" Torpedo kimamin jirage guda 5 yayinda suka fito suna atisaye a tekun Atlantic sai jiragen sukayi batan dabo.
Jiragen sun fito ne daga Lauderdale, Florida a Disamba 5, 1945 domin kaddamar da atisaye na tsawon awa biyu a bakin Atlantika sai suka gamu da gamonsu duka jami'an dake cikin jiragen su 14 babu labarinsu har gobe.
Haka kuma a wannan rana da aka tura masu aikin ceto don su lalubo Flight 19 da jirginsu mai taken PMB mariner BuNo 59225 mai dauke da jami'ai 13 suma sun hallaka har yau babu labarinsu.
Sai kuma jirgi na uku kirar Douglas C-54 ya tarwatse a tsibirin kusa da Florida ranar 3, july 1947 yayinda matukin jirgin ya kasa sarrafa shi.
Sai jirgi na hudu mai suna Avro Tudor G-AHNP star tiger ya bace bat ranar 30 January 1948 dauke da matukan jirgi 3 da fasinjoji 27.
Sai kuma jirgi na biyar kirar Douglas C-3 mai number NC16002 mai dauke da ma'aikatan jirgi guda 3 da fasinjoji 36 wanda shi kuma ya hadu da nasa gararin bacewar a ranar 28 December 1948.
Wadannan kadan daga cikin adadin jiragen ruwa dana sama daga suka bace a wannan tsibiri kenan.
Me masana suka ce game da wannan wuri?
To akwai dai hasashe na mutane daga fannonin ilimi daban daban dangane da kokarin bayyana abinda ya ke a wannan wuri na bamuda.
Misali masana ilimin sinadarin da ke janyo abu daga sama zuwa kasa wato (force of gravity) suna ganin cewa a wannan yankin na bamuda akwai wani mayan karfe na musamman wanda yake da karfin fizgo duk wani abu da ya yi kokarin ratsawa ta wannan wuri komai girmansa kuwa.
![]() |
| Al'amarin tsibirin bermuda akwai abin tsoro matuka. |
Kuma dazarar ya zukoshi tun da yake a tsakiyar teku ne to shi kenan shifa halaka ta gabbata a gareshi, kuma ba za’a taba jin duriyarsa ba.
Su kuwa masana ilimin falaki wato Astronomers suna ganin cewa, wannan wuri na bamuda da ke a cikin teku wata kafa ce ta zuwa sauran duniyoyi, saboda haka duk abin da ya bi ta cikinsa wato kamar dai ya tafi wata Duniyar ne ba ta Dan-adam ba.
Su kuma masana ilimin falsafa philosophy a nasu ra'ayin, wurin na bamuda wata katafariyar fadar shedan ce inda duk abin da yayi kokarin tsallakata zai halaka.
Wannan al’amari dai ba wai magana ce ta hadari ko tsautsayi ba, magana ce ta bacewa bat a nemi abu ko sama ko kasa a rasa, saboda haka kenan batun sanin kididdigar yawan mutanen da suka halaka ko kuma yawan dukiyoyin da aka rasa abu ne mawuyaci.
Wannan al’amari dai ba wai magana ce ta hadari ko tsautsayi ba, magana ce ta bacewa bat a nemi abu ko sama ko kasa a rasa, saboda haka kenan batun sanin kididdigar yawan mutanen da suka halaka ko kuma yawan dukiyoyin da aka rasa abu ne mawuyaci.
Marubuta da dama kowa ya zage dantse don ganin yayi bincike ya bankado hakikanin abinda ke hallaka jama'a a wannan tsibiri amma abin yaci tura daga baya sai a ga cewa sam bincikensa ba shine daidai ba.
Me marubuta suka wallafa a game da wannan tsibiri?
To wadannan kadan daga cikin ire-iren binciken da aka dade ana yi kenan a wannan bagire mai ban al'ajabi na bermuda.
Sai dai kawai maganar dai a nan itace cewar wannan wuri da ake kira da suna Bamuda triangle gaskiya ne akwai shi, amma har yanzu duniya bata tabbatar da ainihin ko menene a wannan wuri ba.
Sabon bincike na wannan karni ya fayyace rudanin tsibirin Bermuda
Masana ilimin kimiyya na wannan karni sunyi ruwa sunyi tsaki sun gano musabbabin abinda ke faruwa a tsibirin Bermuda sun karyata zantukan da aka dade ana yi akai na cewa akwai mu'ujizar dake zama sanadin batan dabo na jiragen sama dana ruwa.
Sunce kuma babu wata alakar birinin fatalwoyi na atlantis a tsibirin, kuma babu batun aliens wato bakin halittu masu saukowa daga sama a cikin jirginsu wanda a kimiyyance ake kira UFO.
sa'annan sunce batun da ake cewa wai a nan fadar shedan take sun musanta hakan sun kuma tabbatar da musabbabin abinda ke faruwa a wannan yanki mai tsohon tarihi.
Me masana kimiyyar zamani suka bankado a wannan tsibiri?
To kamar yadda muka sani wannan zamani da muke ciki shine kankat ta fannin kaiwa makura wajen tsananin kwarewa a kimiyya babu wani zamani a baya da ya kai wannan zamani namu kayan aiki da bincike na kimiyya.
Dan haka ba abin mamaki bane dan a wannan karni an sami bakin zaren warware matsalar da aka shafe shekaru aru-aru a baya ba a warware ba, lallai abin ba zai zo da mamaki ba.
Masanan sunce: babban abinda ke kawo rudani a wannan tsibiri ba komai bane illa sauyin yanayi na weather dake faruwa a yankin.
![]() |
| Hoton da hukumar NASA ta nado kenan ya bayyana yaddda wasu siffofi suka bayyana saman teku masu kama da hexagonal shapes sune air bombs |
Tun sa'adda tauraron dan Adam na hukumar NASA ya nado hotuna na musamman a tsibirin an gano abubuwa masu yawa, inda aka gano gajimare wanda tsayinsu yakai mil 20 zuwa 55 da suka ratsa tekun. Mahaukaciyar iskar dake kadawa tsayinta ya kai kafa 45. An gano cewa gajimaren sunada mikakkun kuibi (straight edges) sabanin yadda gajimare suke a markwade kuma a warwatse (randomly) bisa al'ada.
... to me hakan ke nufi kenan?
Wani masanin ilimin taurari Randy cerveny ya kara da cewa: "Tabbas hotunan da tauraron dan Adam din ya nado bakon abu ne kuma abin al'ajabi ne, wadannan siffofi wanda suka bayyana a saman tekun ainihin bama-baman iska ne. Sun samo asali ne daga wani curin sinadarin iska da ake kira microbursts sune suke fashewa ko bindiga yayinda iskar dake saukowa daga cikin gajimare ta daki saman teku nan take sai wasu igiyoyin ruwa dana iska wato (waves) su bayyana sai su fara sarkafewa da juna cikin kankanin lokaci sai su murtuke saman ruwan.
Duk abinda ya fada cikin wadannan bama-baman iskar nan take zasu fizgo shi sa'annan su lankwame shi zuwa cikin karkashin teku sai ya nutse.
Wannan shine sabon bincike na masana ilimin kimiyya da suka kaddamar a tsibirin Bermuda tsibiri mai ban al'ajabi.
To amma duk da haka akwai bukatar fadada bincike gami da tantacewa don tabbatar da sahihancin wannan ikirari na masana ilimin kimiyya, ta yadda mai yiwuwa wannan ya zama shine abu na karshe wanda ka iya warware wannan turka-turka na tsibirin bamuda wanda yaki ci yaki cinyewa.
References
- "The Loss Of Flight 19". Department of the Navy, Naval Historical Center. Archived from the original on July 9, 1997.
- ^ Harro Ranter (3 July 1947). "ASN Aircraft accident Douglas C-54G-1-DO Skymaster 45-519 Florida coast, USA".
- ^ G-AHNP Aviation Safety Network – Avro 688 Tudor 1 G-AHNP
- ^ NC16002 Aviation Safety Network – Douglas DC-3DST-144 NC16002
- ^ G-AGRE Avro 688 Tudor Mk.1 G-AGRE c/n 1253 – Jack McKillop
- ^ "The Milwaukee Sentinel November 20, 1949". google.com. Retrieved 15 July 2017.
- ^ Aviaiton Safety database
- ^ "ASN Aircraft accident Martin P5M-1 Marlin 127705 Bermuda". Retrieved 3 March 2021.
- ^ Harro Ranter. "ASN Aircraft accident 08-JAN-1962 Boeing KB-50K Superfortress 51-0465".
KARANTA WANNAN: ► Mecece Tauraruwa Mai Wutsiya?
Kada ku manta kuyi sharing ga abokanku a social media domin suma su amfana








0 Comments