Wadannan Sune Hanyoyin Da Za Ka Kare Wayarka Ta Android Daga Ransomware


Wallafar YusufWeb Tech

Menene Ransomware?

Ransomware wata irin muguwar manhaja ce (malware) da masu kutse (hackers) ke amfani da ita wajen kulle wayar mutum ko kuma ɓoye bayanansa. Bayan ta kulle wayar, sai ta nuna saƙo tana neman a biya kuɗi kafin a buɗe ta.

A kwanakin nan, irin waɗannan hare-hare suna ƙaruwa musamman ga masu amfani da wayoyin Android.

Ta Yaya Ransomware Ke Shiga Wayarka?

Ransomware na iya shiga wayarka ta hanyoyi daban-daban, kamar:
- Sauke manhajoji daga shafukan da ba a yarda da su ba.
- Shiga links da ba ka yarda da su ba.
- BuÉ—e fayilolin APK daga mutane ko WhatsApp group da ba ka sani ba.
- Amfani da tsohuwar Android wadda ba ta samun sabunta tsaro (Security patches)
- Danna tallace-tallacen bogi daga wasu shafukan yanar gizo. 

Alamomin Cewa Wayarka Ta Kamu da Ransomware

Idan ka lura da É—aya ko fiye daga cikin waÉ—annan alamomi, akwai yiwuwar wayarka ta kamu:
- Wayar tana kullewa ba tare da izinka ba.
- Ana nuna saƙon neman kuɗi.
- Ba ka iya shiga Settings ko wasu apps.
- Wayar tana sake kullewa duk lokacin da ka buÉ—e ta.
- Ana hana ka amfani da wayar yadda ya kamata.

Hanyoyi 10 Na Kare Wayarka Daga Ransomware


1. Sauke Apps Daga Google Play Store Kawai
Ka guji sauke apps daga shafukan da ba ka yarda da su ba ko kuma APK daga mutane marasa tabbas. 

2. Kar Ka Shigar da APK Ba Tare da Tabbatarwa ba
Kafin ka girka APK, ka tabbatar da cewa daga amintaccen tushe yake. 

3. Sabunta Wayarka Akai-akai
Sabbin Android updates suna gyara matsalolin tsaro da masu kutse ke anfani da su. 

4. Sabunta Apps
Kar ka bar apps É—inka tsofaffi. Sabunta su akai-akai domin samun sabbin gyaran tsaro.

5. Yi Amfani da Google Play Protect
Ka tabbatar cewa Google Play Protect yana kunne. Yana binciken apps domin gano waÉ—anda ke da haÉ—ari. 

6. Kada Ka Danna Kowanne Link
Idan ka samu link daga wanda ba ka sani ba ko saƙon da ya yi maka shakku, kada ka buɗe shi.

7. Yi Backup Akai-akai
Ajiye hotuna, bidiyo da takardu a Google Drive ko wani wuri mai aminci. Idan wani abu ya faru, ba za ka rasa muhimman bayananka ba. 

8. Kula da Izinin Apps
Kada ka bai wa kowace manhaja izinin Administrator ko Accessibility sai idan ka san abin da take yi. 

9. Ka Yi Amfani da Kullewar Allo
PIN, Password ko Fingerprint na ƙara kare wayarka daga amfani ba tare da izininka ba.

10. Guji Wayoyin da Aka Yi Wa Root
Sai dai idan kana da cikakken ilimi, root na iya rage kariyar tsaro ta Android.

Idan Wayarka Ta Kamu da Ransomware Fa?

Idan ka ga alamun ransomware:

- Kada ka biya kuÉ—in da ake nema.
- Kashe haÉ—in Intanet idan zai yiwu.
- Nemi taimakon ƙwararren mai gyaran wayoyi.
- Idan kana da backup, ka yi amfani da shi bayan an magance matsalar. 

Kammalawa

Ransomware na daga cikin manyan barazanar tsaro ga masu amfani da Android a yau. Amma da bin ƙa'idojin tsaro, kauce wa apps marasa tushe, da sabunta wayarka akai-akai, za ka iya rage yiwuwar kamuwa da wannan matsala sosai.

Ka tuna cewa riga-kafi ta fi magani.

Idan Wannan Labarin Ya Amfane Ka Kayi sharing ga abokanka domin su ma su kare wayoyinsu.

Domin samun ƙarin darussa kan Android, kwamfuta da fasaha, ci gaba da bibiyar YusufWeb Tech.