Kamar yadda muka sani a al'adar rayuwa bazai yiwu kullum a zauna lafiya ba, dole sai watarana jarabta ta rashin lafiya ta sami abu muddin yanada rai, ba ko shakka wannan zance haka yake, to suma kaji akwai cututtuka masu tarin yawa wadanda ke addabarsu. 

Ciwon kaji shine babban kalubalen da duk mai kiwon kaji ke fuskanta. Yanzu ga kadan daga cikin ire-iren wadannan cutuka da alamunsu da kuma yadda za a magancesu ta hanyar gudanar da riga-kafi. Gasu kamar haka:

1. Marek's Disease (MD): Wannan cutar virus ce mai addabar kaji, tana hanasu girma. Wannan cuta tana shafar matan kaji ne kadai da kuma yan tsaki masu tasowa yan sati 6 zuwa 20.

Alamun cutar: Shanyewar kafafuwa da fuka-fukai. Idan kaza ta kamu da wannan ciwo zakaga ta kwanta da kuibin jikinta yayinda kafafuwanta sun mike daya gaba daya baya kamar wannan hoton na kasa

Alamun Marek's disease kenan

To da zarar kaga wannan to kasani cewa kazarka ta kamu da marek's disease sai ka hanzarta daukar mataki don gudun kada cutar ta watsu ga sauran kajin masu lafiya. A wasu lokutan ma kaji da yawa sukan mutu ta sanadiyyar wannan ciwo batare da sun nuna wata alama ba. Wannan cuta mai saurin yaduwa ce ta iska dan haka tanada hadari sosai.

Maganin Cutar: Ita wannan cuta batada wani magani face riga-kafi, shine kadai matakin dakile cutar kafin faruwarta, lallai ya zama wajibi a rika yiwa kaji riga-kafi na wannan mugun ciwo mai illata kaji akai-akai.

2. Newcastle Disease: Wannan cuta a wani kaulin ana kiranta da (Ranikhet disease) itama cutar virus ce wanda tana faruwa ne ta dalilin kwayar cutar paramyxoviruses wannan cuta akwai mai sauki-sauki akwai kuma mai tsanani sosai, tana yaduwa ta hanyar shakar iska, abinci, ko ruwan shansu.

Alamun cutar: Alamun cutar mai tsanani sune mutuwar kaji bagatatan. Wasu alamun kuma sun hada da rashin karfi, koren kashi mai ruwa-ruwa, yawan kwanciya, jemewar fuska, murdewar wuya da kuma shanyewar kafa duk alamu ne da suke bayyana ga kajin da suka kamu da wannan cuta ta Newcastle disease. Alamun cutar ga kaji layers kuwa zakaga suna saka kwai wanda bawon kwan mai rauni ne bashi da kwari, ko kuma su rika yin kwai mara bawo kwatakwata daga karshe sai su daina yin kwai yayin da cutar tayi tsanani.

Yadda cutar Newcastle ke murde kan kaza ya koma sama 


Maganin cutar: Newcastle disease bata da wani sahihin magani kawo yanzu, sai dai matakan kariya na riga-kafi, da tsaftace gonar kiwon kaji a kowane lokaci.

3. Infectious bronchitis: Ita wannan cutar tana saurin yaduwa tamkar wutar daji, itama virus ce ta sanadiyyar coronavirus tana bazuwa ta cikin iska da kuma cudanya da kayayyakin da cutar ta shafa kamar kwandon dauko kaji.

Alamun cutar: Sune zakaji kaji suna minshari, nishi, yawan tari da attishawa, yoyon hanci da  kashi da jemewar fuska, baÆ™i-baki a bakinsu sai kuma karancin saka kwai ko kuma raunin bawon kwai idan kaza mai ciwon infectious bronchitis ta saka.

Yadda bronchitis ke kama kaji tamkar darba a bakin su.


Maganin cutar: Kamar dai sauran cutukan dake baya itama wannan babu wani sahihin maganinta sai dai ka dage wajen basu antibiotics. Sannan kuma sai ka hanzarta kai wadanda suka kamu waje busasshe mai dumi-dumi don murmurewa. Amma a wasu gonakin kajin akwai masu kokarin baiwa kaji wani shayin dumame na maganin gargajiya wadanda suke ikirarin wai yana aiki wajen warkar da kaji masu fama da wannan cutar.

4. Fowl pox: Itama wannan cutar virus ce mai yaduwa ta hanyar ciwon dake jikin kaji wato rauni yayin da sukayi gogayya da juna, kuma tana iya bazuwa ta cikin iska sannan kwari suna iya yada ta kamar irin su sauro.

Alamun cutar: Da zarar kaga alamun wani baki-baki a fatar wuya ko kafafuwa ko murar majina ta hanci, kin saka kwai, fitar wata kumfa-kumfa a gefen ido ko kuma farin abu ajikinsu to alamu ne na wannan ciwo.

Alamun cutar Fowl pox


Maganin cutar: Tunda virus disease ce babu wani kwakkwaran maganinta sai dai kaci gaba da kulawa da basu antibiotics da multivitamins a ruwan shansu. Domin kariya ga wannan ciwo ka kula wajen yaki da sauro a muhallin kaji da kuma riga-kafi na Fowl pox vaccine.

5. Botulism: Wannan muguwar cuta ce mai tsanani sosai wanda ta samo asali ne daga botulism toxin wanda bacterium clostridium botulinum ke haifar wa. Tana haddasa raunin jiki da shanyewar jikin kaji. Kaji suna kamuwa da wannan ciwo yayinda suka sha ruwa wanda ya cudanya da kwayar cutar botulism toxin.

Alamun cutar: Da zarar kaga kazarka jikinta ya fara shanyewa kuma tana wahala wajen numfashi to alamun botulism ce sannan gashinsu zai rika zuba nan da nan. Wannan cuta tana saurin kashe kaji cikin yan awanni.

Alamun cutar botulism

Maganin cutar: Hanzarta ka nemi maganin botulism antitoxin mai tsada a shagunan sayarda magungunan kaji. Idan kayi nasarar gane wannan ciwo da wuri to sai ka sami cikin cokali daya na Epsom salts ka gauraya da 3 cl na ruwan dumi sai ka baiwa kazar. Haka zaka ci gaba da bata sau daya a kullum. Insha Allah za a sami waraka cikin gaggawa. Allah yasa mu dace.

Wannan kadan daga cikin ire-iren cututtuka da suke addabar kaji kenan, akwai cututtuka masu yawan gaske wanda bazai yiwu mu kawo su duka ba. 

Da fatan kuna jin dadin wannan shafi namu, muna fata Allah yasa ku amfana da abinda muke rubutawa a wannan shafi, idan kuna da tambaya ko neman karin bayani zaku iya tuntubar mu ta comment section. Mun gode.