WACCE ILLA DUMAMAR YANAYI KE YIWA GONAKIN KAJI?

Dumamar yanayi dai za’a iya danganta shi ne da karuwar zafi ga kajin da ake kiwo a gonaki. Wannan na nufin tsananin zafi fiye da wanda aka saba gani a lokuta mabanbanta.

Kaji kan rage cin abinci a lokutan zafi, ka ga wannan zai shafi abin da ake sa ran samu daga kajin da ake kiwo kenan; zai shafi girmansu, zai shafi yawan tsoka da kwai da za’a samu da kuma yawan kamuwa da cututtuka saboda karancin sinadarai masu bayar da garkuwa ga lafiyar jiki.
Yanayin dumamar yanayi na haifar da karuwar zafi da ke haura ma’aunin zafi digiri 30 na kalsiyos. Duk wannan na haifar da raguwar nauyin kaji da karuwar mutuwarsu.

Kuma idan makiyayi ya lura zai ga idan ruwan sha kaji yayi zafi, za su rage shan ruwa da cin abinci mai yawa. Yanayin kuma zai rage yawan kwai da kananan kaji gidan gona (naTurawa).

Bugu da kari, karuwar yanayin zafi na haifar da cututtuka, wanda ke saka gonakin kaji da dama cikin hatsari saboda yawaitar mutuwar kajin da raguwar amfanin da kajin ke samarwa ta hanyar kwai da Nama, wanda kuma a karshe manomi ko makiyayi ne ke fuskantar wannan asara.

TO MENENE ABIN YI A GONAKIN MU A YAU?

Sigar ma'aunin zafi da yakamata a samar ga kaji kanana

Albishirinku! Akwai matakai na kan-da-garki ko riga-kafi da ya kamata mai kiwon kaji ya dauka a gonakin kaji domin rage mutuwa ko asararsu da ake kiwo sakamakon karuwan zafi.

Akwai bayanai da muka gabatar wa makiyaya kamar ku a taruka daban-daban da ziyarceziyarcen da muka kai gonakinsu a baya.

Wasu daga cikin masu kiwon kajin sun nuna mana matakan da suke dauka domin kare kajinsu daga illar dumamar yanayi, ko sauyin yanayi, domin rage asarar kajinsu, kuma muna shawartar ku, ku dauki irin wadannan matakai.

Ta Yaya Za’a Rage Illar Zafi a kan Kajin da ake Kiwo ?

Yadda yanayin zafi ke raguwa da hauhawa ga kananan kaji masu tasowa

A rage kiwon kaji masu duhu ko bakake domin zafi na saurin shigarsu  Samar da kafofin iska wadatacciya a dakunan kaji  Idan da hali a kara yawan kajin da ake kiwo irin su ‘yar shika rowan kasa da nau’in FUNAAB alpha (‘yar Abekuta), ko kuma fararen kaji da masu haske domin zafi baya saurin shigarsu.


               

KARANTA WANNAN: ►Sana'ar Kiwon Kifi A Saukake