Bayani daki-daki game da yadda ake hada abincin kaji


Ga duk mai kiwon kajin gidan gona yana bukatar sanin yadda zai rainesu cikin sauki kuma cikin koshin lafiya ba tare da fuskantar wata matsala ba.

Dama ma'anar kiwo shine salon ciyarwar da bada isasshiyar kulawa ga abinda ake kiwatawa zuwa wani mataki ko zuwa wani lokaci. To a bangaren kiwo kuwa abinci shine jigo wajen inganta rayuwa ko mu ce shine ma rayuwar saboda dole sai da abinci rayuwa zata tabbata.

Idan muka zo fannin kiwon kaji akwai dangogin abinci mabanbanta wadanda ake ciyar da kajin gida gona, wato akwai ire iren abinci na zamani da kuma na gargajiya, wadanda kowa zai iya hadawa a gida da kansa. Haka zalika akwai wanda ake ciyar da manya da kuma fannin wanda ake ciyar da yan tsaki masu tasowa, haka kuma akwai irin wanda ake ciyar da yan kwai (wato layers) da kuma yan nama (wato broilers). Yanzu dai a takaice ga bayaninsu nan daki-daki a kasa.

SINADARAN DA A KE HADA ABINCIN KAJIN LAYERS


Ka tanaji wadannan abubuwa a bisa ma'aunin kididdiga na (kilogram)

(a) ~ Garin masara (maize meal) 49kg

(b) ~ Waken soya (soya beans) 19kg

(c) ~ Abincin kifi (fish meal) 13kg

(d) ~ Dusar masara (maize bran) 14kg

(e) ~ Farar kasa (limestone powder) 5.9kg

Duka idan ka hada za a sami abincin kaji mai nauyin kilo dari 100kg kenan

Sinadaran hada abincin kaji masu kwai (layers)


SINADARAN DA A KE HADA ABINCIN KAJIN BROILERS


Nemi wadannan sinadaran

(a) ~ Tsakin masara (cracked corn) 110kg

(b) ~ Soyayyen waken soya (roasted soya) 68kg

(c) ~ Oats mai nauyin 11kg

(d) ~ Garin alfalfa (alfalfa meal) 11kg


(e) ~ Garin kifi ko qashi 11kg


(f) ~ Hodar aragonite (calcium powder) 4.5kg

(g) ~ Fertrell nutri-balancer 6.8kg

Idan ka hada duka za ka sami abincin broiler mai nauyin kilo 230kg

1. Bayanin yadda ake hada abincin Kaji yan kwai wato (layers)


Bayan ka tanaji duk abubuwan da muka jero, sai ka sami babban bokiti ko wani mazubi babba sai ka zuba adadin sinadaran a bisa ma'aunin kilograms Garin masara (maize meal) 49kg, Waken soya (soya beans) 19kg, Abincin kifi (fish meal) 13kg, Dusar masara (maize bran) 14kg, Farar kasa (limestone powder) 5.9kg Sai ka hada ka cakuda da chebur (shovel) ka tabbatar ka juya har zuwa kasan kwantenan yadda kowane sanadari zai narke, idan ka kammala sai ka rika diba kana zubawa a mazubi ana bukatar kowane kaza a kalla ya sami 0.28 pound wato (0.13kg) na adadin abincin kowace rana. Wannan shine bayanin yadda ake hada abincin kaji masu kwai a takaice.

2. Bayanin yadda ake hada abincin Kaji yan nama (broilers)


Kada ka manta sinadaran hada abincin broilers sune, Tsakin masara (cracked corn) 110kg, Soyayyen waken soya (roasted soya) 68kg, Oats mai nauyin 11kg, Garin alfalfa (alfalfa meal) 11kg, Garin kifi ko qashi 11kg, Hodar aragonite (calcium powder) 4.5kg, Fertrell nutri-balancer 6.8kg (wadannan sinadaran zaka samesu a kantin saida magungunan kaji)

Haka idan kazo hada abincin broilers sai kabi duk matakan da aka bi wajen hada abincin layers sai dai akwai banbancin kamar haka

1. Ka ware Tsakin Masara (cracked corn) da soyayyen waken soya (roasted soya) ka hadasu a mazubi guda ka cakuda sosai.

Bayan haka sai kuma ka dauko sinadaran Oat 11kg, garin alfalfa shima 11kg sai garin qashi 11kg sai ka zuba a cikin kwantena wanda ka riga ka hada tsakin masara da waken soya sai cakudasu gaba daya ka juya sosai yadda zai ji sosai.

Yanzu kuma sai ka dauko sinadaran aragonite da nutri-balancer ka zuba ka cakuda ka jujjuya da kyau.

wadannan sune matakan hada abincin kajin broilers wadanda idan har aka basu irin wannan abincin to cikin kankanin lokaci zakaga yadda zasu yi girma da kuma koshin lafiya saboda sinadaran suna da romon protein a cikinsu wanda suke taimakawa wajen gina jiki.


Kada ka manta ana bukatar kowace kaza ta broiler ta sami abincin daya kai 0.6 pounds wato 0.27kg a kullum.

Bayan haka ka tabbata ita kwantenar daka zuba abinci tanada murfi mai kyau in har kwantena me kyau ce to zaka iya ajiye wannan abincin kajin har tsawon kimamin wata shida ba tare da ya lalace ba.


Muna fata wadannan bayanai zasu taimaka ma sosai wajen kiwon kaji cikin sauki.

             


KARANTA WANNAN: ► Illoli Da kuma Amfanin Hasken Rana Ga Dan Adam


Kada ku manta kuyi sharing ga abokanku a social media domin suma su amfana