Matakan zabar jinsin kifi mafi dacewa don kiwo
Wannan shine fagen da yafi wuyar sha'ani musamman ga wanda bai taba harkar kiwon kifi ba, saboda akwai ire-iren jinsin kifaye da yawa dan haka dole mutum ya tabbatar ya sami cikakkiyyar kulawa wajen zabar irin kifin da ya dace a kiwata ba tare da an tafka asara ba.
Saboda haka sanin irin kifin da ya dace a noma yanada matukar muhimmanci. Yanzu zamu yi bayani akan jinsin kifi wadanda muka fi mu'amala dasu a kasarmu wato Tilapia da Catfish (boko).
To akalla munada jinsin kifaye kamar haka
1. Tilapia
2. Salmon
3. Tuna
4. Eel
5. Catfish
1. Mu Fara da karfasa (Tilapia).
Kifin Tilapia ya fi kowane irin kifi saukin noma, kuma ana cin Tilapia a kusan ko ina a fadin duniya.
Wannan ya saka su a cikin jerin kifaye da manomansu aka fi samun riba. Wannan kifi na jurewa ire-iren ruwa da kuma yanayi, da karfin iya rayuwa cikin sinadarin ammonia mai yawa, da kuma jure karancin sinadarin iska wato “oxygen”, kuma kifin Tilapia suna da juriyar rashin lafiya, ba kamar sauran kifaye ba.
Bayan haka lallai ka sani cewa:
a. Tilapia na bukatar ruwa mai yanayin 84 digiri farenhai (29 digiri selsiyo). Suna iya rayuwa a cikin ruwan dake da yanayin 64-90 F (18-32 C), amma zasu iya mutuwa idan ruwan yayi sanyi kasa da 50 digiri.
b. Akwai Tilapia iri-iri, kamar Bava, Blue, Nile sune suka fi dacewa da wanda yake so ya fara kiwon su a bayan gidansa.
2. Catfish (tarwada)
Wannan jinsin kifi mai suna Catfish yanada matukar saukin sha'ani wajen kiwo da kuma kawo riba mai dinbin yawa, saboda kifi ne mai juriya da kuma iya rayuwa cikin kowane irin tafki karami ko babba.
Idan har kana bukatar cin gajiyar noman kifi cikin sauri to wannan shine kalar kifin da zaka zaba, sukan yi girma cikin watanni 15 zuwa 21 wanda zasuyi girman 0.454 kg (454 grams) suna matukar son abinci irin su shinkafa da waken soya (soya beans).
Haka nan shima wannan kifi yana da jinsi kusan 3000, amma sanannu sune:
(i) Yellow blue head
(ii) flathead
(iii) black blood head
(iv) channel
(v) walking
(vi) brown Catfish
Yanayin ruwan kiwon Catfish
Temperature a kududdufin kiwon catfish ana bukatar 28.30C zuwa 300C.
Dandanon ruwan wato (ph) kada ya wuce 6.5 zuwa 8.5. Dan haka a rika dandana ruwan akai akai don gudun lalacewa.
Ka tabbatar a kowane lokaci tafkin a tsaftace yake kada ka bari wasu shara ko ganyaye su rika fadawa cikin ruwan, ka tabbatar ka kiyaye kananan yara zuwa kusa da tafkin kifi, don gudun kada su rika dibar shara da duwatsu suna jefawa wanda hakan zai iya kawawo kifayenka matsala.
Ciyar da kifaye abinci
To yanzu tunda mun zabi irin kifin da zamu kiwata har ma mun riga da mun zuba su a tafki, sai kuma batun ciyarwa.
To kamar dai yadda muka sani, ciyarwa shine jigo a kowane irin abinda mutum zai ajiye ya rika kula dashi a matsayin kiwo, dole sai an tanaji abinci mai nagarta wanda zai dace da bukatar kifayen da kake kiwatawa.
Kifaye suna bukatar abinci isasshe kamar yadda dan Adam yake bukata, musamman abincin mai dauke da sinadarai masu gina jiki.
Kasani cewa kifaye suna matukar son cin (algae) wato gansa-kuka ko lobobi musamman tarwada suna bukatarsa sosai, yi dabarun da algae zai rika taruwa cikin tafkin kifayen. Idan kana bukatar haka to sai ka rika zuba kashin kaji ko fertilizer wa algae din to nan da nan zasu rika habbaka, su kuma kifaye sai su rika kalaci dasu.
Haka nan suna cin kananan kwari da kuma tana. Yana da kyau ka siyo pellets musamman wanda akayi da waken suya, masara ko kuma shinkafa.
Cikakkiyyar kulawa gami da tanadar abinci mai nagarta zai taimaka kwarai wajen samun inganci da kuma samun koshin lafiya ga kifayenka, kuma zai taimaka musu wajen saurin girma da hayayyafa cikin kankanin lokaci.
Ciyar da kifaye ya fi kyau da safe ko da rana. Sa'annan kada ka bari wani abinci wanda ba nasu ba ya rika shiga tafkin saboda zai iya rubewa ya zama tamkar guba a garesu wanda zai iya haifar musu da babbar matsala.
Sa'annan kuma idan kaje siyan abincin kifi ka tabbatar ka siyo wanda ya dace da irin jinsin kifin da kake kiwatawa, saboda akwai ire-iren abinci na jinsin kifaye mabanbanta.
Matakan kariya daga cututtuka da muggan kwari don kiyaye lafiyar kifayenka
Ka tsaftace tafkin kifi kullum domin bada kariya daga barazanar kamuwa da cututtuka ko wasu kwari wadanda zasu iya cutar da kifayenka. Bayan haka ka rika neman shawara wajen kwararru masana harkar noman kifi yayinda kake son bada magani ga kifaye marasa lafiya.
Kada ku manta kuyi sharing ga abokanku a social media domin suma su amfana
0 Comments